1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Cholera na ta ƙara barkewa a Angola.

May 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buxn

A ƙasar Angola, matsalar barkewar cutar na ta Cholera, sai kara muni take yi. Rahotannin baya-bayan nan da muka samu daga birnin Luanda sun ce, kusan mutane dubu da ɗari 3 ne suka rasa rayukansu, sakamakon kamuwarsu da cutar. Richard Veerman, shugaban ƙungiyar likitocin nan ta Medecin sans Frontière, a ƙasar, ya ce yawan rayukan da suka salwanta takamaimai zai fi haka. Ya ƙara da cewa, miliyoyin jama’a na huskatar kasadar kamuwa da cutar. Sabili da haka ne ya yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta ƙara mai da himma, wajen shawo kan yaɗuwar cutar.

Cutar dai, wadda ta fara ɓarkewa a birnin Luandan, a cikin watan Fabrairun da ya gabata, a halin yanzu tana yaɗuwa ne kamar wutar daji zuwa sauran yankuna na kasar.