1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuba ta samu sabon shugaban kasa

Salissou Boukari
April 19, 2018

Sabon shugaban kasar Kuba Miguel Diaz-Canel da aka zaba domin ya maye gurbin Raul Castro a wannan Alhamis din ya sha alwashin ci gaba da akidar nan ta juyin-juya hali da kuma kawo sauye-sauye.

https://p.dw.com/p/2wMO4
Kuba Wahlen Miguel Diaz-Canel
Hoto: Reuters

A jawabinsa na farko a matsayinsa na shugaban kasar ta Kuba, Miguel Diaz-Canel, ya ce al'ummar kasar Cuba ta damka masa jagorancin kasar domin ya dasa daga inda aka taya a wannan lokaci mai cike da tarihi da kasar ke fuskantar sauye-sauye inda ya ke cewa "na dauki nauyin da ya rataya a kaina na wanda aka zaba tare da tabbacin cewa dukannin masu ra'ayin juyin-juya hali na kasar Kuba ko ma wane mukami muke da shi, ko ma wane aiki muke yi."

'Yan majalisar dokokin kasar ta Kuba ne dai suka zabi Miguel Diaz-Canel a matsayin sabon shugaban kasar na tsawon shekaru biyar wanda ake iya sabuntawa bayan kawo karshen wa'adin mulki na biyu na Shugaba Raul Castro Ruz.