Cu gaban rikici a kasar Burma | Labarai | DW | 27.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cu gaban rikici a kasar Burma

Sojoji a kasar burma sun sake harbi kann masu zanga zanga a kokarinsu na tarwatsa dubban jamaar kasar da suka fito suna adawa da gwamnati a babban birnin kasar Rangoon.Wadanda suka ganewa idanunsu sunce akalla mutum guda ya fadi bayan harbe harben amma baa san wane irin rauni ya samu ba.Rahotanni sunce akalla mutum 70,000 sukayi kunnen uwar shegu da gargadi da sojojin suka yi na daukar kwararan mataki muddin dai masu zanga zangar basu koma gidajensu ba.Zanga zangar ta yau ta biyo bayan wani hari ne da sojojin suka kai kann guraren ibada na Buddha inda suka tsare sufaye kusan 200,wanda hakan ya janyo kiraye kiraye daga kasa da kasa ga gwamnatin Burma da ta bi abin a hankali.

PM Burtanixa Gordon Brown yace daukar matakin soji ba shine

A halinda ake ciki kuma majalisar taraiyar turai tayi kira ga kasashe Rasha da China da su dakatar da kawo cikas ga yunkurin komitin sulhu na yin Allah wadai da yin anfani da karfin soja wajen dakatar da zanga zangar .