1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cristina Fernandez Kichner: sabuwar shugabar ƙasar Argentina

October 29, 2007
https://p.dw.com/p/C15S

A Ƙasar Argentina, an zaɓi matar shugaban ƙasa mai barin gado, Cristina Fernandez Kichner a matsayin sabuwar shugabar ƙasa, tun zagaye na farko.

A jawabin farko da ta gabatar jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen, Cristina Fernandez, ta yi godiya ga al´ ummar Argentina gaba daya, mussamman mijin ta, shugaba Nestor Kichner, sannan ta yi kira zuwa gare domin sun hada don ginin ƙasa.

Ita shugaba ta farko mace da aka zaɓa a wannan ƙasa.

A tunanin da dama daga masu sharhi a kann harakokin siyasar Argentina ,zaɓen Fernadez Kichner ba abun mamaki ba ne ,ta la´kari da farin jinin ta, a fagen siyasar ƙasar da kuma kyaukyawar rawar da mijin ta ya taka, wajen haɓaka tatalin arzikin ƙasar Argentina.

Yar takara da ta zo sahu na 2, Elisa Carrio, ta rungumi ƙaddara da wannan kayi da ta sha.