CR ta fara ziyarar kwanaki hudu a YGT | Labarai | DW | 15.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

CR ta fara ziyarar kwanaki hudu a YGT

Sakatariyar harkokin wajen Amurka CR, ta fara wata ziyarar kwanaki hudu izuwa yankin gabas ta tsakiya.Ana sa ran ziyarar zata kasance sharar fage ne ga shirin Amurka na gudanar da taron sulhu a tsakanin Israela da yankin Palasdinawa.Jim kadan da saukar ta filin jirgin saman Tel Aviv na Israela, kafafen yada labarai sun rawaito CR na shakkun cimma tudun dafawa, a lokacin wannan taro da Amurka ke shirin daukar nauyin shiryawa. Tuni dai CR ta fara ganawa da shugaba Ehud Olmert da kuma ministan tsaro na kasar Ehud Barak. Bugu da kari CR ta kuma sadu da faraministan yankin na Palasdinawa Salaam Fayaad.Sakamakon tattaunawar da bangarorin biyu dai na nuni da cewa har yanzu akwai sauran tsalle a gaba, game da burin da aka sa a gaba. Kafin dai kammala ziyarar, CR an shirya cewa zatza ziyarci kasashen Masar da kuma Jordan