Cote D′ivoire za ta aike da dakarunta a arewacin kasar | Labarai | DW | 19.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cote D'ivoire za ta aike da dakarunta a arewacin kasar

Gwamnatin Cote D'ivoire na kokarin yin riga kafi na tashe tashen hankula dangane da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a gudanar

default

Laurent Gbagbo,

Gwamnati a kasar Cote D'ivoire ta yi shelar aikewa da sojoji dubu biyu zuya yanki arewacin kasar.

Wannan addadi dake zaman kari ga jam'ian jandarma dubu takwas dakuma tsafin bradan kungiyar yan tawayyen na Force nouvelle dake a can jibge,zai taimaka ga kiyaye tsaro a jajibirin zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a gudanar a karshen wannan wata na nuwanba idan allah ya kaimu.

Zaben wanda za a fafata tsakannin Alassane Ouattara na yankin arewaci dakuma futacen shugaban kasar wanda ya zo na farin a zagayen farko wato Laurent Gbagbo na cike da izgili.

Dangane da abinda ka iya biyo bayan bayyana sakamakonsa,

a halin da ake ciki majalisar dnkin Duniya ta ce zata aike da karin dakarunta na kiyaye zaman lafiya kamar dubu tara

Mawallafi : Abdurahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu