Corea ta Arewa ta ƙauracewa tebrin shawarwari a game da rikicin makaman nuklea | Labarai | DW | 13.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Corea ta Arewa ta ƙauracewa tebrin shawarwari a game da rikicin makaman nuklea

A wani abu mai kama da game kai, ita ma ƙasar Corea ta Arewa, ta bayyana aniyar ta, ta cigaba da mallakar makaman nuklea.

Mataimakin praministan ƙasar ne, Kim Kye Gwan, ya bayyana hakan sahiyar yau, a birnin Tokyo na ƙasar Japan.

Yau ne, a ka tanadi ganawa, tsakanin wakilan ƙasashen da ke shiga tsakanin wannan rikici, da su ka hada da, Rasha Amurika, China da Japon.

Wakilin Amurika Christopher Hill, Amurika ya bayyana wa manema labarai cewar, babu zato babu tammaha,Kim Kye Gwan, ya kaurcewa tebrin shawara, ya kuma yi barazanar kasar sa za ta ci gaba da mallakar makaman kare dangi.

Sauran kasashen sunyi, kira ga tawagar Corea ta kudu, da ta dawo, a ci gaba da tantanawa.