1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Congo ta haye kujerar shugabancin AU

Zainab A MohammadJanuary 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu2C
Chief Obasanjo,shugaban AU mai barin gado.
Chief Obasanjo,shugaban AU mai barin gado.Hoto: AP

Bayan kai ruwa rana adangane da kasar da zata jagoranci kungiyar gamayyar Afrika a taron kolinta a birnin Khartum,a yanzu an cimma yarjejeniyar bawa kasar Congo jagorancin kungiyar.

A yini na biyu kuma na karshen taron kungiyar gamayyar Afrika a birnin Khartum din kasar Sudan ,shugabannin kungiyar sun amince da bawa kasar Congo kujerar shugabancin,kana kasar Sudan wanda ta zame mai masaukin bakin zata karba a shekara ta 2007,wanda ya dinke barakar hana bawa Khartum din wannan matsayi a yanzu.

Kokarin da sudan din tayi domin samun wanna kujera ya ci tura,saboda rashin goyon baya data fuskanta kkannmatsaloli da lardin Darfur ke ciki a yanzu haka ,yankin da kungiyar ta AU keda dakarun kiyayae zaman lafiya dubu 7 dake kokarin ganin cewa an samo bakin zaren warware rikice rikice dake addaban wannan yanki.

Shugaba Denis Sassou-Nguessou,wanda ya shugabanci Congo daga 1979 zuwa 1992 kana ya sake karbar ragamar mulki bayan kifar da gwamnati a shekarata 1997,shine ya karbi kujerar shugabancin kungiyar ta Au daga shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeria,a yau wadda ke kasancewa ranar karshe na wannan taro na Khartum.

Shugaba Balaise Compaore na Burkino Faso,dake zama daya daga cikin wakilan kasashe bakwai da aka nada dfomin warware matsalar shugabancin kungiyar daya mamaye wannan taro,ya fadawa manema labarai cewa har yanzu akwai matsaloli da sudan din ta kasa magance su.

Amma suna fatan cewa nan da shekara ta 2007,sudan din zata cimma bakin zaren warware wadannan ringimu na cikin gida da take fama dasu,wanda zai bata daman hayewa wannan kujera.

A bara nedai gwamnatin Sudan din ta rattaba hannu kann yarjejeniya sulhu domin kawo larshen yakin basasa daya dauki shekaru 21 yana gudana a kudancin kasar,sai dai rikicin lardin darfur daya kashe mutane sama da dubu 300 kana ya watsar da kimanin million biyu na cigaba da addaban yammacin kasar,wanda ya zuwa yanzu an kasa gano bakin zaren warware shi.

Daya daga cikin ministocin Sudan din daya fito daga kudanci Deng Alor,yace sanin kowa ne tun da farko cewa bazaa bawa sudan kujeran shugabancin wannan kungiya ba.

Yace ya ragewa Sudan din ta yi gyaran harkokinta na cikin gida ,domin ya bata sukunin karbar ragamar shugabancin wannan kungiya a shekara mai zuwa.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin jamaa sukayi gargadin cewa bawa Sudan wannan kujera ,kamar sakawa gwamnatin Omar Hassan El-Bashir ne da ,da Amurka kemasa zargin kisan kiyashi a darfur,kana zai kashe darajar kungiyar ta gamayyar Afrika.

Masu kare hakkin jamaan dai sunyi nuni dacewa shima shugaba Denis Sassou-Nguessou,bawai yana da wani tarihi mai kyau kann kare hakkin biladama a congo ba,sai dai bazaa kwatantashi dana El-Bashir din sudan ba.

Kasashen masar da libya dai sun nemi a bawa sudan wannan kujera ,amma kasashen yammaci da kudancin Afrika suka nuna adawa da hakan.