Condoleezza Rice ta zargi Syria da Iran da rura wutar zanga zangar adawa ga kasashen turai | Labarai | DW | 13.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Condoleezza Rice ta zargi Syria da Iran da rura wutar zanga zangar adawa ga kasashen turai

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta yi kira ga kasashen Iran da Syria da su nuna dattako a game da zanga zangar dake cigaba aukuwa a kasashen musulmi sakamakon zanen batanci ga Annabi Muhammad S.A.W. Condoleezza Rice wadda ta zargi kasashen Iran da Syria da shirya zanga zangar adawar ga yammacin turai tace lamarin na nema ya gagari kundila. Zanga zangar dai na cigaba da yaduwa a kasashen musulmi na duniya. A waje guda kuma makabartun musulmi kimanin guda ashirin da biyar ne aka lalata a yammacin Denmark. P/M kasar Anders Fogh Rasmussen ya yi Allah wadai da wannan dabiá yana mai cewa zaá hukunta wadanda suka lalata makabartun.