Condoleezza Rice ta isa Birnin Kudus a ziyarar aiki ta biyu cikin mako daya | Labarai | DW | 29.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Condoleezza Rice ta isa Birnin Kudus a ziyarar aiki ta biyu cikin mako daya

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta sauka a Isara´ila a matakin farko na sabon rangadin da take kaiwa yankin GTT karo na biyu cikin kasa da mako daya. Rice ta ce zata gudanar da shawarwari masu tsauri da shugabannin yankin, musamman a danagne da shirye shiryen girke dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen duniya a kudancin Libanon. Shugaban ´yan Hisbollah Hassan Nasrallah ya ce Rice ta koma yankin na GTT don ta gindayawa Libanon wasu sharudda a matsayin wani shirin kirkiro wani sabon yankin GTT, kamar yadda Amirkawa ke so. A cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan telebijin Nasrallah ya ce ziyarar ta Rice ba komai ba ne illa biyawa Isra´ila bukatun ta. Nasarallah ya ce Isra´ila na da shirin dakatar da yakin domin tana tsoron abin da ke boye, to amma Amirka ce ka kara angiza ta ta ci-gaba da yakin. Nasrallah ya ce dakarunsa zasu ci-gaba da harba rokoki cikin Isra´ila, idan kasar ra Bani Yahudu ba ta daina kai farmaki akan Libanon ba.