Condoleeza Rice ta gana da ministoci 8 na kasashen larabawa | Labarai | DW | 01.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Condoleeza Rice ta gana da ministoci 8 na kasashen larabawa

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta gana da ministocin harkokin wajen kasashen larabawa guda 8 kafin babban taronsu da zasu gudanar nan gaba,akan halin da ake ciki a yankin Paladinawa,Iraqi da kuma Lebanon.

Ministocin na larabawa sun jaddada bukatar dake akwai ta magance matsaylar yankin Paladinawa wadda itace ummul abaisin duk wani rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da baiyana goyon bayansu ga shugaba Mahmud Abbas ,sun kuma mika goyon bayansu gwamnatin kasar Lebanon a kokarinta na sake gina kasar.

Kasashen sun hada da Jordan da Masar da kasashe 6 na majalisar hadin kai ta yankin Gulf.

Tun farko a jiya lahamis rice ta kai ziyara yankin Palasdinawa da na Israila inda ta tattauna da shugaba Mahmud Abbas da kuma firaminista Ehud Olmert,kann yiwuwar komawa tattaunawar zaman lafiya.