Condoleesa Rice ta gana da takwarorin ta na EU a Brussels
December 8, 2005Talla
Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice,ta gana yammancin jiya, da takwarori ta na kungiyar gamayya turai a birnin Brussels, jim kadan bayan taron kungiyar tsaro ta NATO, da ta halarta.
Rice, ta yi bayyani dalla dalla, a game da zargin da ke wa hukumar liken assiri ta Amurika, na cewar ta yi anfani a assirce,da filayen saukar jiragen sama na wasu kasashen turai domin jiggilar pirsinioni, da kuma tsarewa da gana ukuba, ga wanda ta ke zargi da aiyuka ta´adanci ,a wasu gigajen kurkuku a turai.
Ministan harakokinnwajen kasar Belgium Karel De Gucht ya bayyanawa manema labarai cewa, ministocin na EU baki daya sun gamsu da hasken da Rice ta bada a game da wannan batu.