Cocin Jamus ta bayyana matsayinta game da Terry Jones | Siyasa | DW | 09.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cocin Jamus ta bayyana matsayinta game da Terry Jones

Coci a Jamus ta yi Allah wadai ga matakin Terry Jones na ƙona Alƙur´ani mai tsarki

default

Zanga-zanga a Afganistan game da Terry Jones

Wata Coci a Jamus ta yi Allah wadai da shirin da tsohon shugaban ta Terry Jones ke yi na ƙona Alƙur´ani mai tsarki a ranar Asabar, domin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu a harin 11 ga watan Satumba. Jones ya kafa Cocin ne sanda ya fara zuwa Jamus a shekarun 1980 a matsayin mai yaɗa bishara, amma ya rabu da cocin a shekarar 2008 domin a cewar sa, sun yi hannun riga.

Mataimakin shugaban alummar krista da kebirnin Kolan  Stephen Baar, ya ce a lokacin da Terry Jones ke Fastor a wurin, ya riƙa wa'azin cewa su  karanta Bible/Linjila a kowani lokaci, ya ce bai taɓa nuna tsautsauran ra'ayin 'yan ta kifen da ya ke nuna wa a sabon cocin sa ta Florida ba inda har ya yi kira ga mabiyan sa da su ƙona Alƙurani mai girma

 "Na farko dai ina so in bayyanyar a fili cewa cocin mu na Allah wadai da Terry Jones. Ba mu da wata hurɗa da shi yanzu, kuma muna nuna baƙin cikin mu sakamakon shirin sa na ƙona Alƙurani mai girma. A matsayin cocin sa na daa, mun yi Allah wadai da wannan ra'ayin na sa."

A lokacin da Jones ya zo Jamus, yana da shekaru 24 kuma ya yi fiye da shekaru 30 yana shugabancin cocin, wanda a lokacin da zai tafi tana da mambobi fiye da dubu ɗaya.

Stephen Baar ya ƙara da cewa, yayin da ya ke paston ya fi bai wa kan shi mahimmanci fiye da koyarwar Bible/Linjila da mahimmancin su.

"Wa'azin shi kuma sai ya zama kamar ba na addinin krista ba, sai ya fi ba da ƙarfi wajen nuna kansa da ikon da ya ke da shi da kuma matsayin da ya kai a cocin. Daga ƙarshe sai muka ce ya tafi, babu faɗa ba tashin hankali, muka ce ya tafi, kuma sai ya tafi"

Ko da yake Baar ya ce ba a sami wani saɓani ba ko tashin hankali da Jones zai tafi, wasu ba su amince da hakan ba.

Brigitte Baetz  wata 'yar jarida mai zaman kanta ta ce akwai dangantaka tsakanin halin sa a daa da kuma yan

 " A hukumance, babu wani bayyananen dalili na tafiyarsa, amma wannan saboda mabiya cocin na sa basu so su fito fili su yi maganar paston su bane. ko a wajen cocin, mutane sun san shi da irin wannan tsatsauran ra'ayin na takife. Ya bayyana Kolan a matsayin dandalin uƙuba kuma ya gaya wa mabiyarsa cewa zasu fuskanci azabtarwa daga waɗanda ba su zuwa cocin sa. Sa'an nan kuma ya taɓa ƙaryar cewa shi likita ne, wannan ma a kotu aka ƙaryata shi, kuma na tabbata abubuwa da yawa zasu fito yanzu".

Baetz ta ƙara da cewa mutun ne wanda ba ya so mabiyan sa suna ƙalubalantar sa, kuma ba abubuwan da suke so ya ke yi ba. Ta ce tana ganin cewa fadar White House za ta hana shi, kuma shuwagabanin duniya zasu soke wannan ƙona Alƙur´anin mai girma da ake barazansar  yi ranar asabar.

Tun da Jami'an tsaro na gida ba za su iya kare wannan abun daga faruwa ba, da alamar cewa ƙaramar coci a Florida zata jawo tashin hankali a dangantakar da ke tsakanin Muslmi da ƙasanshen yamma a  duniya baki ɗaya.

Mawallafi: Pinado Abdu

Edita:Ahmed Tijani Lawal