1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ciwon zuciya ne ya kashe Milosevic

March 13, 2006

Bayanai na likitoci na nuna cewar Milosevic ya mutu ne sakamakon ciwon zuciya

https://p.dw.com/p/Bu1B
Slobodan Milosevic
Slobodan MilosevicHoto: AP

An saurara daga wata mai magana da yawun kotun ta kasa da kasa tana mai yiwa manema labarai bayani a yammacin jiya lahadi cewar:

Likitocin sun tabbatar da cewar ciwon zuciya ne ya kashe Slobodan Milosevic. Likitocin sun gano wasu illoli guda biyu a zuciyarsa, wadanda kuma sune suka yi sanadiyyar mutuwarsa.

Da farko dai wasu likitoci daga kasashen Netherlands da Serbiya ne suka yi tsawon sa’o’i da dama suna binciken gawar marigayin dake da shekaru 64 da haifuwa. An dauki hoton binciken nasu saboda gudun zargin magudi ta la’akari da jijita-jitar da aka rika yayatawa tun bayan mutuwarsa ranar asabar da ta wuce. A kuma jiya lahadi an saurara daga bakin daya daga cikin lauyoyin Milosevic yana mai fada wa manema labarai cewar:

An miko mini wani kundin binciken da aka gudanar a ranar 12 ga watan janairun da ya wuce, wanda ke nuna cewar an gano burbushin wasu magunguna a cikin jinin Milosevic, wadanda bisa al’ada ake amfani da su wajen jiyyar masu fama da cutar kuturta da tarin fuka.

Wadannnan magunguna, in ji lauya Zdenko Tomanovic, su ne suka karya tasirin magungunan kayyade hauhawar bugun jini da marigayin ya saba amfani da su. Hatta bayan binciken gawar tasa da aka yi, wannan zargin yana nan daran-dakau ba a gusar da shi ba. Ba kuma tabbas ko wani ne ya mika masa wannan maganin ko kuwa shi kansa ne ya rika hadiyarsa tattare da sanin abin da zai biyo baya.

An dade dai Milosevic na kokawa a game da rashin wata nagartacciyar hanya ta kiwon lafiyarsa a kurkukun na MDD dake Schveningen a kasar Netherlands, inda ya fi kaunar da a kai shi Mosko don neman magani, amma kotun ta kasa da kasa tayi fatali da wannan roko da aka gabatar mata a ‘yan watannin da suka wuce. Har yau kuwa, bayan mutuwar fuj’a da Milosevic yayi, babbar mai daukaka kara Carla del Ponte na kan bakanta cewar shawarar kotun ta kin amincewa da tura tsofon dan kama karyar neman magani a Mosko abu ne da ya dace saboda kotun ta dauki nagartattun matakai na kiwon lafiyarsa. Da dai a ‘yan watanni masu zuwa ne za a kammala shari’arsa, kuma ga alamu tare da hukuncin daurin rai-da-rai a gidan kurkuku, kamar yadda Carla del Ponte ta nunar.