Ciwon zazzabin cizon sauro a Habasha | Siyasa | DW | 29.12.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ciwon zazzabin cizon sauro a Habasha

A yanzu haka dai an fara daga hakurkura tare da rashin amincewa ga wani mataki da kungiyar nan ta Medicine sans Frontiers ke dauka na samar da magungunan zazzabin cizon sauro ga kasar Habasha inda Gwamnatin kasar tace sam kada kungiyar ta fara bayar da wannan magani ga wadanda ke kwance walau a Asibiti ko kuma a gida a sabili da kamuwa da wannan cuta .Bincike dai ya nunar da cewa a yanzu haka a kalla yan kasar kimanin miliyan 15 sun fada wannan tarko a kasar ta habasha sabili da wannan barazana da cutar ke haifarwa ga yan kasar baki daya Kamar dai yarda iministan lafiya na kasar Kebede tadesse ya soki lamirin kungiyar nan ta MLF na shige gona da iri domin cigaba d a jirkitar da hankalin yan kasar kann samaR DA WANNAN MAGANI GA YAN KASAR :Yace saanin kowane a yanzu kungiyar ta fara gudanar da wani kanfe na wasa da hankalin yan kasaer wanda yace ko kadan gwamnati ba zata lamunta ba .Tadessa yace kasa komai girmanta ko kuma talaucinta bai dace a yi wasa da hankalin taba a dangane da samar da koshin . lafiya ga yan kasar a kowane lokaci ba .A wani taron manema labaru da ministan ya gudanar a yau litinin cewa yayi Habasha zata cigaba da bin sau da kafa kann dokokinta na tabbatar da kiwon lafiya ga yan kasar batare da haifar da rudani ba Yace matakin da kungiyar ta MLf ta dauka na anfani da sabnbin magungunan ga yan kasar a wani mataki na gwaji sam bai dace ba kuma gwamnati ba zata amince da hakan ba .To sai dai a hannu guda kungiyar na kira ga gwamnatin kasar data dauki mataki na mika wuya domin cimma manufar samarwa da yan kasar magani cikin ruwan sanyi .A cewar kungiyar wannan maganin ya sami amnincewar hukumar WHO ,hukumar dake kula da fannin lafiya ta mDd Kungiyar dai na mai raayin cewa magungunan da yan kasar ke anfani da shi don maganin cizon saura ya fara yin laasar wanda yasanya samart da wannabn magungunan ga yan kasar a halin yanzu ..A wani taron kasa da kasa da aka gudanar a Adis a babna a watan satumban daya shude na masana ilimin kimiyya da fasaha sun koka bisa yawan samun rahotanni na zazzabin cizon sauro a kasar ta habasha wanda yasa dople ne a dauki mataki na shawo kann lamarin cikin gaggawa ..To sai dai duk da wannan halin da ake ciki minista Tadesse yace ba abu ne mai yiwuwa ba anfani tare da gwajin magani kann marasa lafiya don kawai cuta ta barke a kasar .Wani bincike dai ya nunar da a kalla mutane sama da miliyan 45 ne ke cikin wani irin hali na ni kyasu a sabili da wannan cuta cikin alummar kasar miliyan 70 .daya daqa cikin shugabannin wani yankin Oromia ya shaidawa rediyon kasar cewa a yanzu cutar da malaria ta fara taaazzara a yankin baki daya .Yace idan kuwa akai wasa to babu shakka mutane da dama zasu bakunci lahira a yan kwanakin nan .Idan dai baa mantaba a watan oktoban daya gabata MDd ta kaddamar da wani asusu na tallafi ga kasar ta Habasha na kimanin Dala Miliyan 6 domin yaki da ire iren wadannan cututtukan a kasar

 • Kwanan wata 29.12.2003
 • Mawallafi Mansour BB
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvmt
 • Kwanan wata 29.12.2003
 • Mawallafi Mansour BB
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvmt