1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cire shingen kasuwanci a Afirka

Umar Ahmad Abubakar | Zainab Mohammed Abubakar
November 29, 2017

Shugabannin hukumomin kwastam na kasashen yammaci da kuma tsakiyar Afirka na yin dubi kan hanyoyin bunkasa kasuwanci a tsakanin kasashen wadanda ke cigaba da fuskantar matsalolin tattalin arziki

https://p.dw.com/p/2oSy7
Marokko Berber Markt in Kalaat M'Gouna
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Elshamy

 Kasuwanci tsakanin kasashen na nahiyar Afirka ya tsaya ne a kashi 12 cikin 100 abunda kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU ke yunkurin daga shi zuwa kashi 23 cikin dari a shekara ta 2020 ta hanyar kawar da duk wani shinge na kasuwanci a tsakanin kasashen.

To sai dai kasuwanci a nan na fuskatar matsaloli da dama, kama da ga cin zarafin yan kasuwa daga jami'an yan sanda dama tsauraran matakan ketara iyakokin kasashen. Antoinette Angono ya shafe shekaru ashirin yana safarar kayan abinci daga kamaru zuwa kasar Gabon.

kasuwanci tsakanin kasashen Afirka ya cigaba da zama koma baya, abun da Gilbert Muchanga, Daraktan kasuwanci da masana'antu na kungiyar hadin kan ksashen Afirka AU ke cewa matsalar ita ce kasashen Afirka na samar da kayayyakin da ake fitarwa zuwa ketare amma babu wani abu da ake gani a kasa.

Jami'an kwastam a Afirka dai na aiki tukuru wajan habaka kasuwanci tsakanin kasashen, abun da ke zama wani matakin farko na kungiyar tarayyar Afirka ta AU wajen kawar da duk wani shingen kasuwanci tsakanin kasashen, kamar yadda yake kunshe a cikin yarjejeniyar inganta kasuwanci dama samarda kasuwa ta bai daya.

Irin wadannan matakan ne babban daraktan hukumar kwastam na kasar kamaru Fongot Edwin Nuvaga ke alfahari da su inda kasashe makwabtan kamaru,  wato Chadi da da jamhuriyar Afirka ta tsakiya a yanzu ke amfani da wani tsarin bin sahun kayayyaki na zamani da kasar ke amfani da shi mai suna NEXUS.