1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cire rigar kariya ga 'yan majalisar Turkiya

Leteefa Mustapha Ja'afar/ASMay 17, 2016

Majalisar dokokin kasar Turkiya ta tafka muhawara dangane da batun cire wa 'yan majalisun dokokin kasar da ake zargi da aikata laifuka rigar kariya.

https://p.dw.com/p/1IpTk
Symbolbild Türkei Ankara Parlament
Hoto: picture-alliance/dpa/Str

'Yan majalisa da dama ne daga cikin mammabobin majalisar dokokin kasar ta Turkiya wannan lamari zai iya shafa. Masu fashin baki dai na ganin mahukuntan na Turkiya sun kirkiri wannan mataki ne a kokarin da suke na ganin bayan 'ya'yan jam'iyyar adawar kasar da ke goyon bayan Kurdawa ta HDP a majalisar.

Türkei Ankara Präsident Recep Tayyip Erdogan
Erdogan ya ce cire rigar kariya ya zama wajibi don hukunta masu goyon bayan 'yan ta'addaHoto: Getty Images/AFP/A. Altan

A ranar Juma'a 20 ga wanannan wata na Mayu da muke ciki ne dai ake sa ran majalisar za ta amince da sabon kundin tsarin mulkin da a cikinsa aka tanadi sabuwar dokar cire rigar kariyar ga 'yan majalisun da ake zargi da marawa 'yan kungiyar 'yan awaren PKK ta Kurdawa baya. Wannan batu dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mahukuntan Turkiyan ke ikirarin yakar 'yan kungiyar 'yan awaren Kurdawa ta PKK da suka ayyana a matsayin kungiyar ta'adda.

To sai dai a hannu guda wasu na ganin gwamnatin kasar na son amfani da wannan dama ce ta cire rigar kariyar wajen muzgunawa 'yan adawa amma shugaban Turkiyya din Racep Tayyip Erdogan ya musanta hakan inda ya ke cewa:

'''Yan majalisun na amfani ne da rigar kariyarsu wajen mara wa kungiyar 'yan ta'adda baya kawai. Ya zama wajibi 'yan majalisa da kuma fannin shari'a su dau mataki a kan 'yan majalisun da ke zama tamkar garkuwa ga kungiyoyin 'yan ta'adda."

In har majalisar ta amince da wannan sabuwar doka dai, to tabbas shi ma shugaban jam'iyyar adawa ta HDP mai goyon bayan Kurdawa Selahattin Demirtas zai fuskanci hukunci. A wani martani da ya maida ya ce wannan doka mataki ne na sabawa ka'idojin dimokaradiyya kana ya kara da cewar:

Türkei Selahattin Demirtas Pressekonferenz
Shugaban jam'iyyar HDP mai adawa Selahattin Demirtas ya ce shirin cirewa 'yan majalisa rigar kariya bit da kulli ne ga 'yan adawaHoto: Reuters/S. Kayar

''Al'ummar kasar za su rasa fatan da suke da shi kan 'yantacciyar dimokaradiyya.''