1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin Makaman Jamus A Ketare

October 15, 2004

Kasashe sama da 100 ne ke sayen makamai kirar Jamus a sassa dabam-dabam na duniya

https://p.dw.com/p/BvfV
Tankin yaki na Leopard 2 kirar Jamus
Tankin yaki na Leopard 2 kirar JamusHoto: dpa

Makamai kirar Jamus na da farin jini a kusan dukkan sassa na duniya, musamman ma motoci da tankokin yaki masu sulke, wadanda galibi aka saba sayar da su ga kasashen kungiyar tarayyar Turai da ta tsaron arewacin tekun atlantika NATO. Idan ba za a manta ba, sai da aka sha famar kai ruwa rana a game da wasu tankokin yaki masu sulke kimanin 36 da aka sayarwa da kasar Saudiyya a shekara ta 1991, kazalika da kuma cece-kucen da ake yi a yanzun dangane da wasu tankokin na dako da ake da niyyar yi wa sojan kasar Iraki damararsu. Wani rahoton cinikin makamai da gwamnatin hadin guiwa ta SPD da the Greens ta gabatar yana kunshe da bayani filla-filla a game da kasashen da suka fi cinikin makamai da Jamus a sassa dabam-dabam na duniya. A lokacin da yake bayani game da haka wani kwararren masanin hada-hadar cinikin makaman dake nan Bonn Michael Brzoska ya ce cinikin ya kan banbanta daga shekara zuwa shekara. Misali a shekarar da ta wuce kasashen Koriya ta Kudu da Girka da kuma Turkiyya sune suka fi yi wa Jamus cinikin makamai, a yayinda a sauran shekarun da suka gabata Isra’ila da Indonesiya suka kasance akan gaba wajen sayen makaman daga Jamus. Akwai alaka ta kut-da-kut tsakanin masana’antun sarrafa makamai na Jamus da kasar Isra’ila. To sai dai kuma a baya-bayan nan gwamnati a fadar mulki ta Berlin ta ki amincewa da cinikin wasu motocin soja masu sulke samfurin dingo 2 da Isra’ilar ta so ta saya daga Jamus. A cikin shekarun 1990 sai da aka sha famar kai ruwa rana akan wasu jiragen karkashin teku da aka gudanar da cinikinsu, saboda ana iya sauya musu fasali domin dakkon makaman kare-dangi. A kuwa halin da ake ciki yanzun kasar ta Isra’ila ta sake bayyana bukatarta ta sayen wasu karin jiragen karkashin tekun daga Jamus. Kasashe da dama a sassan duniya dabam-dabam ke sha’awar sayen jiragen ruwan yaki kirar Jamus. Kasar Indiya na daya daga cikin wadannan kasashe. Kazalika ita ma Afurka ta Kudu ta fara kutsawa sahun gaba, inda nan ba da dadewa ba za a tura mata dimbim jiragen ruwan yaki da ta saya daga kamfanonin Jamus. To sai dai kuma kamar yadda muka yi bayani tun farko kasashen kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO da na kungiyar tarayyar Turai sune suka fi yi wa Jamus cinikin makamai. Dangane da kasashe masu tasowa kuwa, duka-duka abin da suke saya bai zarce kashi 20% na yawan makaman da kamfanonin Jamus ke sarrafawa ba. Daya daga cikin dalilan haka kuwa shi ne koma bayan cinikin makamai da aka samu a kasuwannin duniya baki daya da misalin kashi 40%, a tsakanin shekara ta 2000 zuwa shekara ta 2003, kamar yadda wani bincike ya nunar. A takaice dai kamfanonin makaman na Jamus dake da ma’aikata kimanin dubu casa’in da kuma gudummawar kashi 1% kacal na jumullar abubuwan da kasar ke samarwa a shekara, suna gudanar da cinikinsu a kasashe sama da 100 a sassa dabam-dabam na duniya.