1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin makaman Amurka a Gabas Ta Tsakiya

June 14, 2007

Amurka ce ummal'aba'isin mawuyacin halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya sakamakon taimakon makaman da take bayarwa

https://p.dw.com/p/BtvL

Manufar shugaban na Amurka dangane da karfafa tsaro, musamman a fadar mulki ta Bagadaza dai ta ci tura. Bugu da kari kuma wannan manufar tsofuwa ce da aka saba gani daga shuagabannin Amurka da suka gabata, wadda kuma ba ta taba haifar da da mai ido ba. Amurkan ta tashi gadan-gadan tana taimaka wa ‘yan Sunnin Iraki da makamai, wai domin su fatattaki ‘ya’yan kungiyar Al-Ka’ida daga kasar, bisa zargin cewar su ne ke da alhakin mummunan harin da aka kai baya-bayan nan babban masallacin Samarra, daya daga cikin muhimman wurare masu tsarki na ‘yan Shi’at. Amma fa hakan babban kuskure ne in ji Carsten Kühntopp. Ya ce bata kashin da ake fama da ita tsakanin Hamas da Fatah a zirin Gaza da yaki tsakanin sojan Lebanon da dakarun wata kungiya mai tsananin kishin addini da kuma dauki ba dadi tsakanin ‘yan Shi’at da ‘yan Sunni duk ba su da wata nasaba da juna illa kawai gaskiyar cewa kasar Amurka da kawayenta na shisshigi cikin lamarin tare da taimakawa da kudi da kuma makamai, lamarin dake kara dagula halin da ake ciki. Dangane da Palasdinu, kungiyar Fatah bata taba amincewa da manufar da aka cimma a farkon shekara ta 2006 ba, kuma kasashen Amurka da Masar da Jordan na bata goyan baya ga wannan matsayi nata, suna masu taimaka mata da makamai da kuma kaurace wa Hamas a kokarin ganin cewar kungiyar bata ci gajiyar nasarar zaben da ta samu ba. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda gwagwarmayar kama madafun ikon ta rikide zuwa yakin basasa tsakanin Pasladinawan su ya su. A Lebanon kuwa sojoji ne ke wa wasu daruruwan mayakan musulmi kofar rago a wani sansani na ‘yan gudun hijira tun misalin makonni hudu da suka wuce. Ga alamu kuniyar mai suna Fatah el-Islam ta dade tana samun taimakon kudi daga Saudi-Arabiya a karkashin wata manufa, inda Amurka da kawayenta na yankin mashigin tekun pasha ke taimaka wa dakarun sa kai a kasar Lebanon. Manufarsu ita ce taimaka wa ‘yan sa kai mabiya akidar sunni domin yin daura da Hizballah ‘yar Shi’at. A Irak kuwa Amurka ta shiga yi wa ‘yan sunni damarar makamai bisa fatan cewar zasu taimaka a fatattaki Al-Ka’ida. A takaice a zirin Gaza ana taimaka wa wata gwamnati ‘yar cin hanci, wadda aka karya alkadarinta ta hanyar zaben demokradiyya a yayinda a Lebanon ake rufa wa wata gwamnati baya, wadda akasarin al’umar kasar ke kyamarta. A Iraki kuwa ana ba da taimakon makamai ne wai ko Ya-Allah hakan zata taimaka a cimma zaman lafiya. Wani abin da yakara munana lamarin ma shi ne jahilcin shugaba Bush na Amurka da ya dauki lamarin tamkar fada ne tsakanin kirki da mugunta. Muddin aka ci gaba akan haka Allah ne kadai ya san yadda makomar Gabas ta Tsakiya zata kasance.