1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cinikin makamai tsakanin Rasha da Venezuela

Shugaban Venezuela Hugo Chavez na ziyarar kasar Rasha inda zai sanya hannu kan yarjeniyoyin sayen makamai, wanda ya ta da hankalin kasar Amirka. Yarjeniyoyin sun hada da sayarwa Venezuela jiragen saman yaki samfuri Su-30 guda 30 wanda kudinsu ya kai Euro milyian 790 da kuma helikoptoci guda 30. Amirka wadda ta haramtawa kamfanoninta sayarwa Venezuela makamai, ta bukaci Rasha ta sake yin nazari akan shirin cinikin makaman. Dazu da safe shugaba Chavez ya ziyarci wasu masana´antun kera makamai wadanda ke kera bindigogin Kalashnikov. Wani jami´in gwamnatin Rasha ya ce ana tattaunawa da nufin cimma wata yarjejeniyar bude wasu masana´antu biyu dake kera bindigogin Kalashnikov a Venezuela.