Cinikin makamai tsakanin Libya da Faransa | Labarai | DW | 03.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cinikin makamai tsakanin Libya da Faransa

ƙasar Libya ta sanya hannu akan wata yarjejeniya da Faransa ta sayen tankokin yaƙi na garkuwar makamai masu linzami akan tsabar kudi euro miliyan 168. Wannan dai ita ce cinikayya ta farko da ƙasar Libyan tun bayan cire takunkumin da ƙasashen turai suka ƙaƙaba mata. An sanya hannu akan yarjejeniyar ce da kamfanin ƙera makamai masu linzami na tarayyar turai MBDA, kamfani mafi girma na ƙera makamai a duniya. An kuma kammala wata yarjejeniyar cinikayyar ta kayan sadarwa ƙasar Faransan zata sayarwa Libya da kuɗin su ya kama euro miliyan 128. Dan shugaba Gaddafi Saiful Islam ya shaidawa jaridar Le Monde ta Faransan cewa sakin maáikatan lafiyan nan shidda da libya ta yi a makon da ya gabata, ya share fagen cimma yarjejeniyar makaman tsakanin Libya da Faransa. A hannu guda dai shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya musanta cewa sakin maáikatan lafiyar na da nasaba da yarjejeniyar makaman.