Cin zarafi ta hanyar lalata tsakanin al'umma a Afirka
November 19, 2013Talla
Wannan salsalar na bada labarin Hadiza, Fati da Adams, waɗanda duk suka fuskanci cin zarafi. An kuma nunar da yadda suke rayuwa da illolin da wannan lamari ya haifar da ma wuraren da suke zuwa samun taimako. Duk lokacin da aka tilasta wa mutum yin jima'i ba tare da san ransa ba, an ci zarafinsa ke nan. Wannan irin cin zarafi ya kan afku ne a ɓoye kuma waɗanda abun ya shafa su kan ji tsoron faɗa wa kowa saboda kunya.