1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar cin naman gwangwani da jan nama

Suleiman Babayo / LMJOctober 28, 2015

Tun lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa cin jan nama da kuma naman da aka saka sinadarai mai yawa na kara yiwuwar kamuwa da cutar sankara ake samun martani.

https://p.dw.com/p/1Gw8U
Naman da aka sanyawa sinadaran hana lalacewa
Naman da aka sanyawa sinadaran hana lalacewaHoto: picture alliance/Photocuisine.de

Bangaren kula da cutar sankara na hukumarta WHO ne ya wallafa wannan rahoto da ya nuna yadda yawaita cin jan nama da kuma wanda aka saka masa sinadarai na hana abu lalacewa da wuri ka iya kara yiwuwar kamuwa da cutar ta sankara. Farfesa Sabine Rohrmann masaniya ce a kan cutar sankara a Jami'ar Zurich da ke Switzerland ta kuma ce:

Illar cin nama fiye da Gram 50 a rana

"Abin da muka gano shi ne yawan cin nama da aka sarrafa da sinadarai na kara yuwuwar kamuwa da cutar sankara da kashi 18 cikin 100 idan mutum ya ci fiye da gram 50 a rana"

Yadda a kan sarrafa jan nama
Yadda a kan sarrafa jan namaHoto: BGodunoff - Fotolia

Tuni gwamnatoci suka fara mayar da martani inda ministan kula da abinci da aikin gona na Jamus Christian Schmidt ya bukaci mutane kada su razana, kuma su ci gaba da cin abinci kamar yadda suka saba. Masu wuraren kiwo gami da gidajen sayar da abinci suna cikin masu martani kamar Palma Pazienza a Italiya ta na mai ra'ayin cewa:

Martani kan rahoton na WHO

"Ban yi tsammanin zan sauya yadda nake cin abinci ba, saboda na shafe duk tsawon rayuwa ta ina cin naman da aka sarrafa da sinadarai babu abin da ya faru. Sai dai ma nama da aka sarrafa ya fi lafiya a kan wani abincin. A kauce wa cin nama ko abinci fiye da kima shi ne mafita."

Shi ma Henri Baudet daga kasar Faransa na da irin wannan ra'ayi, ina ya ce:

"A'a ban yi tsammani ba. Ba na tunanin cin wani abu daban. Muddin aka ci abinci mai gina jiki babu matsala. Zan ci gaba da cin nama ko akwai yiwuwar cutar sankara ko babu."

Sai dai a cewar Farfesa Sabine Rohrmann masaniya kan cutar sankara a Jami'ar Zurich da ke Switzerland ra'ayin mutanen na kan hanya.

Yanayin cutar sankara ko kuma Daji
Yanayin cutar sankara ko kuma DajiHoto: Imago/Science Photo Library

Ta ce: "Gaskiyar ita ce ba kowa ba ne idan ya ci naman da aka sarrafa da sinadarai zai kamu da cutar sankara, ko kuma kowanne mai shan taba zai kamu da cutar sankara ta huhu ba. Amma abin da muka gani shi ne yawaita cin nama da aka sarrafa da sinadarai kullum zai iya kara yiwuwar kamuwa da cutar ta sankara."

Shi dai wannan rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi bitar wasu bincike-bincike ne kimanin 800 da aka gudanar kafin ya kai ga wannan matsaya.