Cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Tchadi da yan tawaye | Labarai | DW | 03.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Tchadi da yan tawaye

Gwamnatin Njeimena ta cimma yarjejeniyar sulhu da manyan kungiyoyin yan tawaye hudu a kasar, wanda aka zartar a Tropoli,kuma zasu rattaba hannu akai cikin kwanaki masu gabatowa.Ministan kayayyakin raya kasa na tchadi kuma Adoum Younousmi ne ya cimma wannan yarjejeniya da shugabannin kungiyoyin adawan hudu a kasar Libya ,inji majiyar bangarorin biyu.Shugaban Daya daga cikin kungiyoyin da ake kira UFDD,ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaru na Afp daga turai ta wayan tangaraho wannan matsaya da bangarorin suka cimma yau a Tripoli.Gwamnatin Tchadin dai ta zargi gwamnatin Khartum da taimakawa hadin gwiwar yan tawayen kasar,domin yakar ta.