1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikwan shekara guda da mutuwar Paparoma Jean Paul II

April 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3J

A kwana a tashi, yau shekara guda kenan daidai, da Paparoma Jean paul na 2, ya kwanta dama.

Albarkacin wannan rana, Paparoma Benedikt na 16, da ya gaje sa, ya gabatar da jawabi,cikin karyayya murya, inda yayi yabo, na mussamman, ga ayyukan da mirganyi ya gudanar, a tsawon rayuwar sa,ta fannin samar da zaman lahia, tsakanin alu´mmomi, da addinai daban -daban na wannan dunia.

A ƙalla dubu 100, a ke sa ran , za su hallara a dandalin Saint Pierre, na fadar Vatican, inda an jima kaɗan, domin gudanar da salloli, ga mirganyi jean Paul na.

Dubun dubunan kristoci, mabiya ɗarikar roman katolika, sun ziyarci makwancin sa, domin yi masa addu´a.

Kazalika, a ƙasashe da dama, an gudanar da salloli a wannan rana, ta juyayi da rashin Karol Wojtyla.