1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cika shekaru 20 da hadarin chernobyl

Zainab A MohammadApril 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6o

Kimanin matane 1,500 ne suka halarci adduoi na musamman a birnin Minsk din kasar Belarus,na cika shekaru 20 tare da nuna alhini ga wadanda hadarin tashoshin nuclearnnan na Chernobyl ya ritsa dasu,wanda aka bayyan da kasancewa hatsari mafi muni daya ritsa da wannan kasa.

Majamiar da aka gudanar da wannan adduoi dai,wadanda suka taimaka wajen sake ginin yankin bayan wannan hadarin tashoshin nuclear ne suka ginashi,wanda ya auku akan iyakar kasar da Ukraine dake makwabta.Ministan harkokin tallafi na gaggawa na Ukraine ,Enver Bariyev ya fadawa taron masu nuna alhinin cewa,Ukraine utace da tayi asaran kashi 70 daga cikin 100 na wannan balai daya auku shekaru 20 da suka gabata.yace sama da rabin alummar kasar ne suka jikkata a wancan lokaci.

Mr Enver yace alummomin Ukraine zasu ciga da gudanar da adduoi domin nuna alhini wa dumbin mazauna tsohuwar tarayyar soviet ,da suka fuskanci sakamakon wannan balai daya ritsa da yankin a wancan lokaci.