Cigaban ziyarar jakadar MDD a Zimbabwe | Siyasa | DW | 28.06.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cigaban ziyarar jakadar MDD a Zimbabwe

Da sauran rina a kaba dangane da kammala rushe rushen matsugunnai a Zimbabwe

default

Ayayinda jakadar majalisar dunkin duniya ke cigaba da ziyarar gani da ido,yansandan Zimbabwe sun sanar dacewa suna mataki na karshe na rushe rushen matsugunnen yan kama wuri zauna daya dauki tsawon makonni 5 yana kudana a sassan kasar.

Kakakin yansandan gwamnatin Zimbabwe Wayne Bvudzijena ya fadawa taron manema labaru a birnin Harare cewa suna matakai na karshe na kamala rushe rushen da suke gudanarwa.Yace duk dacewa sun kamala rusa dukkan yankuna da aka umurcesu,akwai sauran kalilan wadanda zaa dada rusawa.

Dangane da waaadin kamala wannan aiki da suka sanya gaba,kakakin yansandan yace babu takamammen lokaci ,domin zasu ciga da ziyartan dukkan yankunan domin tabbatar dacewa jamaa sun bi umurnin su.

A makonni biyar da suka gabata dai yansandan Zimbabwe sunyi amfani da manyan motoci na ruguza gine gine wajen rusa gidaje,shaguna da kasuwanni da matsunai da aka gina babisa kaida ba,a wani shirin da gwamnatin kasar ta kira yaki da miyagun ayyuka.

A dangane da matsin lamban Amurka da Britania nedai sakataren Mdd Kofi Annan,ya nada jakada ta musamman wadda ta isa kasar Zimbabwe tun ranar lahadi,domin ganewa idanunta wannan rushe rushe da kuma illar daya haifar masu matsugunnen.

Bayan isarta a kasar dai Jakada Mdd Anna Kajumulo Tibaijuka ta gana da shugabannin dukkan hukumomin mdd dake Harare,kana ana kyautata zaton cewa zata gana da sugaba Robbert Mugabe kafin ta ziyarci yankunan da aka gudanar da wadannan rushe rushe.

Wakiliyar hukumar raya kasashe masu tasowa ta Mdd dake Zimbabwe Katherine Anderson ta fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa,Jakada Anna tana ganawa na sirri da kwararru na Majalisar dake birnin Harare.

Rahotanni daga Zimbabwen dai na nuni dacewa Ranar da wakiliyar MDD ta sauka a wannan kasa,an gudanar da rushe rushen gine gine a garin Chitungwiza,inda aka bar iyalai da dama ba tare da matsuguni ba.

Kafofin yada labaru na kasar sun ruwaito cewa yansanda sun rusa gidajen saukan baki guda biyar a fadar kasar,ayayinda aka cafke yan Nigeria 6,acigaba da kamfaign din gwamnatin kasar na yaki da yan kama wuri zauna.

A jiya dai jaridun kasar sun rewaito cewa gwamnati na gayyatar yan kwangila ,magina,kafintoci ,domin basu kwangilar sake gina wuraren da zaa tsugunar da wadanda suka rasa matsugunnensu.

Jaridar Herald mallakar gwamnatin Zimbabwe tace kimanin mutane dubu 20 da 477 ne zaa sake bawa filayen gini a wajen birnin Harare,ayayinda gwamnati ke shirin samarda gidaje wanda yawansu yakai million daya da rabi nan da shekaru 4 masu gabatowa.

Mdd dai tace akalla mutane dubu 200 suka rasa matsugunnensu a wannan kamfaign da gwamnatin mugabe ke gudanarwa,ayayinda yan adawa suka cewa adadin wadanda suka rasa matsugunnensu yakai million 1.5.

Ana dai zargin cewa shugaba Mugabe yayi hakan ne amatsayin hukunci wa wadanda sukayi adawa da zaben watan maris dayaba jammiyarsa ta Zanu-Pf nasara,tare da koransu da birni zuwa wajen gari.

Tuni dai shugaban na Zimbabwe yak are wannan rushe rushe dayakeyi,kuma ya samu goyon baya wasu daga cikin wakilai 53 na kungiyar gamayyar Afrika,kungiyar da taki sa baki,domin injita wannan matsalace ta cikin gida.

 • Kwanan wata 28.06.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvb2
 • Kwanan wata 28.06.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvb2