1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban ziyarar Christian Wulff a Turkiyya

October 21, 2010

Shugaban ƙasar Jamus yana ziyarar al'ummar Kristoci a Tarsus

https://p.dw.com/p/Pk7E
Hoto: dapd

A rana ta uku a ziyarar da yake yi a ƙasar Turkiyya shugaban ƙasar Jamus Christian Wulff, ya isa garin Tarsus dake yankin kudancin Turkiyya. Inda ya gana da wakilan majami'un Ɗarikun Protestant da Roman katholika, kazalika da na Armenia, da masu  ra'ayin rikau na Girka da Syria. Wanmnan ganawar dai na da nufin nuna goyon bayan shugaban ƙasar ta jamus wa mabiya addinin Krista dake Turkiyyan. Bugu da kari shugaba Wulff zai halarci sujada ta musamman a majami'ar St.Paul dake birnin na Tarsus, inda nan ne mahaifar waliyyi Paul. Wannan ziyara ta shugaban Jamus a al'ummar Kristocin dai ta zo ne, yini biyu bayan jawabinsa a majalisar Turkiyyan, inda ya bukaci bawa Kristocin ƙasar 'yanci daidai da musulmin Jamus.

Mawallafiya: Zainab Ahmed Mohammed Edita: Abdullahi Tanko Bala