Cigaban ziyara Elbaradei a Korea ta Arewa | Labarai | DW | 14.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cigaban ziyara Elbaradei a Korea ta Arewa

Shugaban hukumar yaƙi da makaman nuklea ta Majalisar Ɗinkin Dunia, Mohamed Elbaradei, ya kai ziyara gani da ido a ƙasar Korea ta Arewa, bayan amincewa hukumomin Pyong-Yang na yin watsi da aniyar mallakar wannan makaman ƙare dangi.

A yayin da ya ke bayana manufar wananziyara Dr Elbaradei na mai cewa:

„Mu na bukatar fahintar abubuwan da su ka shirya gudanarwa.

Ba ma nufin sake komawa baya, ta hanyar sabuwar tanttanwa.

Yanzu ba sai mun ce kaza da kaza mu ke bukata ba, domin mun bayyana bukatocin lokacin tarurukan da su ka gudana“.