1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban somamen dakarun Izraela a zirin gaza

November 6, 2006
https://p.dw.com/p/BudB

Da safiyar yau,Dakarun Izraela sun bindige wani Dalibi Bapalasdine mai shekaru 17 da haihuwa,ayayinda mayakan yahudawan suka shiga yini na shida da kai somame a zirin gaza dake yankin cin gashin kann palasdinawa.Majiyar asibitocin yankin dai sun sanar dacewa Mahmud Ashfari ya gamu da ajalinsa ne kana wasu palasdinawa 9,biyu daga cikinsu yara yan shekara 5-5,sun jikkata ,lokacinda jirgin yakin Izraelan ya harbo makami mai linzami a garin Beit Lahiya,dake arewacin gazan.Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa,dakarun Izraelan sun kai wannan harin wa wani jamiin Hamas,sai dai ya tsira da ransa,ayayinda Linzamin ya tarwatse a kusa da wata motar Bus dake dauke da yara yan makaranta.Bugu da kari Mohammed Taha mai shejkaru 25 da haihuwa,kuma jamiin rundunar sojin kungiyar ta hamas mai mulki,ya gamu da ajalinsa,kana wasu mutane biyu sun jikkata,a wata arangama da dakarun yahudawan izraelan a arewacin Gaza.Da kaddamar da wannan hari a yankin Palasdinawan a ranar larabar data gabata dai,mutane 52 ne suka rigamu gidan gaskiya,da sojin Izraelan guda daya.