Cigaban shirin zaman lafiya a kudancin Sudan. | Labarai | DW | 14.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cigaban shirin zaman lafiya a kudancin Sudan.

Dubban jamaá a ƙasar Sudan sun yi dafifi wajen yiwa tsohon madugun yan tawaye wanda kuma aka naɗa a matsayin sabon gwamnan jihar Blue Nile a kudancin ƙasar, suna masu cewa a yanzu suka san zaá kawo zaman lafiya da cigaba mai maána a yankin kusan shekaru biyu da rabi bayan sanya hannu a kan yarjejeniyar sulhu tsakanin arewaci da kuma kudancin ƙasar. Sabon gwamnan Maliki Agar wanda ada yake riƙe da matsayin Minista mai kula da kadarori da cigaban ƙasa, ya ajiye muƙamin ya karɓi matsayin gwamna, muƙamin da ake zagayawa ta karɓa – karɓa a tsakanin yan jamíyar National Congress Party NCP da kuma tsohuwar ƙungiyar tawaye ta SPLM. Muƙamin da zai rike ta shekara ɗaya da rabi na kasancewa karon farko da jamíyar SPLM zata rike muƙamin gwamna a yankin tun bayan sanya hannu a kan yarjejeniyar sulhun.