Cigaban shariár Saddam Hussain | Labarai | DW | 10.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cigaban shariár Saddam Hussain

A yau ake cigaba da shariár tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussaini tare da mukarraban sa bisa laifin keta haddin alúma. A yau din ne kuma lauyoyin dake kare Saddam din za su gabatar da daáwar su ta karshe. Wata majiya daga kotun ta ce mai yiwuwa ne kashe daya daga cikin lauyoyin Saddam da aka yi ya kawo jinkiri a sauraron shariár na yau. Dan uwan Saddam Barzan al Tikriti tare da wasu jamiai biyar na jamiiyar Baáth za su fuskanci hukuncin kisa idan aka same su da laifi bisa tuhumar da ake musu ta kisan mutane 148 mabiya darikar Shiá a garin Dujail a shekarar 1982. A wani abu dake zama koma baya ga kotun shariár wadda ke da goyon bayan Amurka, wasu yan bindiga dadi a watan da ya gabata suka kashe Khamis al-Obaidi mukdaddashin babban lauya dake kare Saddam bayan da suka sace shi daga gidan sa Bagadaza wanda kuma ke zama mutum na uku daga cikin lauyoyin Saddam din da aka kashe.