Cigaban ruɗani a Iraqi shekaru uku bayan yaki | Labarai | DW | 20.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cigaban ruɗani a Iraqi shekaru uku bayan yaki

A ƙasar Iraqi yayin da ake cika shekaru uku da mamayar da Amurka ta yiwa ƙasar, a waje guda kuma yan siysar ƙasar na cigaba da fuskantar kiki-kaka a yunkurin kafa gwamantin hadin kan ƙasa. Manazarta na baiyana damuwa cewa idan aka kai farmaki a kan dubban mabiya ɗarikar Shiá dake gudanar da bikin Ibada a birnin Karbala akwai yiwuwar faɗawa cikin wani sabon babi na ɗauki ba dadi a tsakanin mabiya dariku. ƙasar Iraqin na fuskantar mawuyacin hali shekaru uku bayan da Amurka ta afkawa kasar, inda a kulli yaumin alámura ke ƙara taɓarɓarewa tun bayan da aka kawar da tsohon shugaban ƙasar Saddam Hussaini. Shugaban Amurka George W Bush ya baiyana Imanin cewa zaá cimma galabar kawar da yan tawaye daga ƙasar Iraqi. Sai dai kuma bayanan na Bush sun saba da raáyin tsohon P/M Iraqi Iyad Allawi wanda ya baiyana halin da ƙasar Iraqin ke ciki a yanzu da cewa tuni ta fada cikin yaƙin basasa.