Cigaba da ziyara Amr Musa a kasar Iraki | Labarai | DW | 24.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cigaba da ziyara Amr Musa a kasar Iraki

Sakataran kungiyar hadin kan larabawa, Amr Musa na ci gaba da ziyara aiki a kasar Iraki.

Babban burin wannan ziyara, da ke gudana , kwanaki kalilan bayan gudanar da zabe, a game na kundin tsarin mulkin kasar Iraki, shine na samun goyan baya, daga al´ummomi daban daban, na kasa, domin shirya wani gagaramin taron hadin kai.

Ya zuwa yanzu, Amr Musa, ya samu goyan bayan da yan shi´a da kuma kurdawa mafi rinjaye a kasar Iraki.

Ya nuna matukar gamsuwa da bayanai, daga shugaban yan shi´a Ayatollah Ali Sistani, da kuma shugabanin kurdawa.

A yayin da ya yi rangadi a yankin Kurdistan, Amrr Musa ya gana da yan majalisar wakilai 111 na wannan yanki.

Wannan itace ziyara ta farko da wani shugaba balarabe ya kai a yankin tun bayan zaben wanan majalisa.

Babban abinda ke kawo cikas a halin yanzu, na shirya taron hadin kan kasar ,shine matsayin yan sunni.

Saidai wannan , ziyara na wakana a cikin yanayi hare haren kunar bakin wake kamar yada a ka saba kullum.

A ranar jiya, mutane 16 su ka rasa rayuka a fadin kasar baki daya.