1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaba da sauraron sharia akan 11 ga watan satumba na 2001

January 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuV5

A yau ne aka koma cigaba da sauiraron shariar dan kasar morokon nan da ake zargi da hannu a harin 11 ga watan satumban 2001,wa Amurka a birnin Hamburg dake nan Jamus.Mounir al-Mutassadeq,dake zama mutumin farko da akia gurfanar kann wannan hari na kunar bakin wake,zai iya samun hukuncin daurin shekaru 15 agidan yari,a wannan zagaye na ukun zaman shariar.A yanzu haka dai yana zaman wakafi na shekaru 7,wanda aka yanke masa a baya.A watan Nuwanban daya gabata nedai aka zartar da wannan hukunci akan Almutassadeq,saboda samunsa da kasancewa dan wata kungiyar tarzoma,da hadin baki da wadanda suka yi garkuwa da jiragen da suka kaiwa Amurkan harin kunar bakin wake.To sai dai azaman shariar da akayi ranar jumaa da maraice,Almutassadeq ya nanata cewa,bashi da wata masaniya dangane da wayancan harin kunar bakin wake.