Ci gaban ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a Amurka | Labarai | DW | 10.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a Amurka

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana ci gaba da tattaunwar da shugaban Amurka George Bush.Shugabannin biyu za su maida hankali ne kan shirin zaman lafiya na yankin Gabas ta Tsakiya da kokarin kawo kwanciyar hanakli a Afghansitan da kuma uwa iba batun nukiliya na Iran.A ranar Jumaa Bush ya karɓi baƙuncin Merkel yana mai baiyana cewa ya na matuƙar girmama ta.Wannan ziyara ta shugabar Jamus wani sabon babi ne a dangantakar ƙasashen biyu tun wani saɓani kan mamaye Iraƙi da Amurka ta yi a 2003.Shugabannin za su kuma tattauna a kan ɗumamar yanayi wanda Merkel ta bada fifiko kansa tun da ta hau mulki a watan Nuwamba na 2005.