Ci gaban ziyarar Merkel a Indiya | Labarai | DW | 01.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban ziyarar Merkel a Indiya

Shugabar gwamnatin Jamus angela Merkel tana shirin kammala ziyarata ta kwanaki 4 zuwa kasar Indiya inda zata gana a yau da wakilan addinai da yan tsirarun kasar a babban birnin kasuwanci na kasar Mumbai.Shugabar ta Jamus tayi anfani da wannan ziyara wajen kara inganta dangantakun ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.A ranar talata Merkel ta gana da firaminista manmaohan Singh a birnin New Delhi.Cikin abubuwa da suka cimma yarjejeniya akai sun hada da ribanya harkokin kasuwanci tsakaninsu da kusan euro biliyan 20 a kowace shekara na tsawon shekaru 5.