Ci gaban ziyara Vladmir Poutine a Afrika | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban ziyara Vladmir Poutine a Afrika

A cigaba da ziyara aikin da ya ke a nahiyar Afrika, yau, shugaban ƙasar Rasha Vladmir Poutine, ya sauka a birnin Casablanca na Marroko.

Wannan itace ziyara farko, da wani shugaban fadar Kremlin ya taɓa kaiwa a ƙasar .

Tawagogin ƙasashen 2, za su anfani da wannan dama, domin tantana batutuwa daban-daban ,da su ka shafi harakokin saye da sayarwa,, ta fannin makashi, kayan massarufi yawan buɗa ido, da dai sauran su.

A ɗaya hannun, Vladmir Poutine, da Sarki Mohamed na 6, za su masanyar ra´ ayoyi, a game da wainar da ake toyawa,a fagen siyasa da na diplomatiar dunia, mussamman halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da kuma batun yaƙi da ta´adanci.

Albarkacin wannan ziyara, shugabanin kampanoni da masana´antu, na ƙasashen 2, za su gana da juna, da zumar bunƙasa shigi da ficin kaya, tsakanin Marroko da Rasha.

Harakokin kasuwanci tsakanin ɓagarorin 2, sun ƙara haɓaka, tun bayan ziyara da Sarki Mohamed na 6, ya kai Rasha a shekara ta 2002.

Kamin ƙasar Marroko, Vladmir Poutine ya yi rangadi a Afrika ta Kudu, inda ya rataba hannu a kan yarjeniyoyin cinikaya, na miliyoyin daloli da takwaran sa, Tabon Mbeki.