1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban ziyara Koffi Annan a nahiyar Afrika.

March 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4z

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, na ci gaba da ziyara aiki a nahiyar Afrika.

Bayan ganawar da yayi jiya, da hukumomin Afrika ta kudu ,a yau Annan ya tantana, da tsofan shugaban ƙasa Nelson Mandella.

Mandella ya kaukyawan yabo, ga rawar da Koffi Annan ,ya taka a Majalisar Ɗinkin Dunia mussamna a game da ayyuka tukuru da ya gudanar, ba tare da nuna wariyar addini ba, to ta launin fata.

Jim kaɗan wannan ganawa, Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinki Dunia ya ziyarci Soweto, sannan ya tashi zuwa Madagascar, inda ya sadu da shugaba Marc Ravalomanana.

Gobe idan Allah ya kai mu, zai issa a ƙasar Congo, domin tantanawa, da shugaban ƙungiyar gamayya Afrika Denis Sassun Nguesso.

A ƙarshen ziyara ta yau, Koffi Annan, da wa´adin mulkin sa ,ke kai ƙarshe a wannan shekara, ya ce zai dawo gida Ghana, domin ci gaba da bautawa Afrika, mussaman, ta fannin ayukan noma, ilimi, yancin yaya mata, da dai sauran ayyuka, da su ka shafi rayuwar yau da kullum.