Ci gaban ziyara Koffi Annan a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 04.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban ziyara Koffi Annan a gabas ta tsakiya

Sakatare Jannar na Majlisar Dinkin Dunia Kofi Annan, na ci gabada ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya.

Bayan ƙasashen Iran da Qatar da ya ziyarata jiya, Annan zai wuce yau zuwa Saudi Arabia.

A ganawar su, da sarki Cheick Hamad ben Khalifa al-Thani, sun tantana a kan halin da a ke ciki a yankin mussamman bayan tsagaita wutar da a ka samu tsakanin Isra´ila da Hizbullahi, da kuma tallafin da ƙasashen larabawa domin tabatar da zaman lahia mai ɗorewa a yankin gabas ta tsakiya.

Jim kaɗan kamin ya sadu da hukumomin Qatar, Koffi Annan ya gana da Mahamud Ahmadinedjad na Iran.

Duk da nacewar da shugaban yayi, a kan matsayin sa, na ci gaba da sarafa makamashin nukleya, ya alkawarta bada goyan baya, ga kundurin MDD, na samar da zaman lahia tsakanin Isra´ila da Hizbulahi.