Ci gaban zanga-zangar adawa da Trump a Amurka
November 11, 2016Talla
A biranen Washington da Baltimore da Philadelphia da New York, masu gangami sun mamaye tituna a wani mataki na nuna bacin ransu kan nasarar da Trump ya samu. Kazalika dubban masu boren ne suka yi cincirindo a Los Angeles da San Francisco da Oakland da California da Portland da Oregon.
Duk da cewar yawancin zanga-zangar na gudana ne cikin lumana, ana gudanar da su ne a kan tituna wanda ke haifar da cikas ga harkokin sufuri da hada-hadar yau da kullum. Rahotanni na nuni da cewar gangamin na ranar Alhamis bai kai wadanda aka yi ranar Laraba ba. A birnin Washington, mutane wajen 100 ne suka yi tattaki zuwa fadar gwamnati ta white inda shugaba Barack Obama ya yi ganawarsa ta farko da mai gadon kujerarsa Donald Trump.