Ci gaban zanga-zanga a Hongrie
October 9, 2006Talla
A ƙalla mutane dubu 20, su ka sake shirya zanga-zanga a yammcin jiya, gaban harabar Majalisar Dokokin ƙasar Hongrie, da ke birnin Budapest.
Masu zanga zangar, na buƙatar Praminsta Ferenc Gyurcsany, yayi murabus daga muƙamin sa.
An shirya zanga-zanga, bisa gayatar shugaban jama´iyar adawa Viktor Orban.
Jam´iyun adawa sun yi alkawarin ci gaba, da matsa kaimi a ko wace rana ,har sai sun cima burin da su ka sa gaba.
Wannan shine rikici mafi muni, da ƙasar Hongrie ta tsinci kanta ciki, tun bayan ƙarshen mulkin komunisanci, a shekara ta 1989.