Ci gaban yaƙi a Libanon. | Labarai | DW | 08.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban yaƙi a Libanon.

A ƙasar Libanon a na ci gaba da ɓarin wuta, tsakanin dakarun gwamnati, da ƙungiyar Palestinawa yan gudun hijira ta Fatah Al-Islam.

Ya zuwa yanzu, a na fuskantar rikici mafi tsanani, a matsungunan yan gudun hijira, na yankin Nahr Al Bared , amma ƙungiyar ta yi barazanar bazuwar yaƙin a wasu sassan Libanon, muddun rundunar gwamnati, bata dakatar da ruwan harsasai ga yankin ba.

Manyan mallumai masu faɗa aji a yankin, sun yi tayin shiga tsakani, ba tare da cimma buri ba.

Gwamnatin Libanon ta alƙawarta ci gaba da farautar yan takifen, har sai sun yi saranda.

A nata ɓangare, ƙasar Amurika, ta ƙara aika tallafi makami, domin karfafa gwiwar ƙasar Libanon, ta yaƙi al´ammuran ta´adanci.