Ci gaban yaƙe-yaƙe a yankin Darfur | Labarai | DW | 16.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban yaƙe-yaƙe a yankin Darfur

Wakilin sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, a yankin Darfur na ƙasar Sudan, ya bayyana damuwa, a game da ci gaban yaƙe yaƙe, da taka haƙoƙin jama´ a a wannan yanki.

A yayin da ya ke bayani ga yan jarida, Jan Pronk, ya ce kullum sahia, sai an gwabza tsakanin, ƙungiyoyi ɗauke da makamai, ko kuma a kai hari ga garuruwa.

Daga watan februaru ya zuwa ranar jiya, a cewar sa, mutane 400, wanda ba su ji ba su gani ba, su ka rasa rayuka, a cikin haren haren, da a kai wa a garuruwa daban-daban.

A dangane da, tarrurukan da ake ci gaba da yi a birnin Abuja Na taraya Nigeria, don maido da zaman lahia, a ƙasar Sudan, wakilin na Koffi Annan, y ace, basu anfana komai ba.

Bugu da ƙari, al´ummomin yankin na ƙara shiga matsanancin hali, na ƙaranci abinci, da cuwarwawata.

Duk da wannan mummuna hali, da ke gudana gwamnatin Sudan, ta bayana adawa, da tura dakarun kwantar da tarzoma, na Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur.