1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban yaƙi a Sri-Lanka

August 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bulu

Rundunar Sri lanka ta ci gaba da amen wuta ta sararin samaniya ga yankunan yan tawayen Tamoul Tigers da ke arewancin ƙasar.

Rundunar gwamnati ta ɗauki wannan mataki, domin rugurguza tulin makamai, da yan tawayen su ka mallaka.

A ɗaya hannun kuma, yan sanda a birnin Colombo ,sun bayyana binciko wani yunƙurin harin ta´danci, da yan tawaye su ka shirya, a cikin kasuwar birnin.

Gwamnatin Sri -Lanka, ta rataya alhakin kai hare haren ta´danci 2, da su ka wakana, a cikin wannan watan, ga yan tawayen Tamoul Tigers.

A tsukin kwanaki 10 da su ka gabata, rikici ya ƙara ƙamari tsakanin ɓangarroin 2, a yankin Jaffna, inda ya zuwa yanzu, mutane kussan 500 su ka rasa rayuka.

Jami´an bada agaji, sun ce a halin da ake ciki , al´umommin yankin, sun shiga halin zullumi, dalili da ƙarancin abinci, da su ke fuskanta.

Rikicin da ke wakana yanzu, shine mafi muni, daga yaƙe- yaƙen da ƙasar Sri-Lanka ta tsinci kanta, a ciki ,yau da shekaru 4 da su ka gabata.