1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban yaƙe-yaƙe a Mogadiscio

May 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuwP

A birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia, a na ci gaba da ɗauki ba daɗi, tsakanin ƙungiyoyin sa kai,masu samun goyan baya daga Amurika, da dakarun kotunan addinin islama.

Daga ranar jiya, zuwa yau, a ƙalla mutane 30 su ka rasa rayuka ,a cikin ɓarin wutar, da ya hada ɓangarorin 2.

Wani mazaunin birnin Mogadiscio, da ya gane wa idon sa yadda rikicin ke wakana, ya bayana shi, da yaƙi mafi muni, da ƙasar ta fuskanta, tun bayan kiffar da shugaba Momahed Siad Bare, a shekara ta 1991.

Ranar juma´a da ta wuce, sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Koffi Annan, yayi kira ga ɓangarorin 2, da su tsaigata wuta, amma wannan kira bayi ba tasiri.

Daga lokacin girka rundunar haɗin gwiwar ƙungiyoyin sa kai,a watan Februaru, kawo yanzu, yaƙi tsakanin wannan ƙungiyoyi da dakarun kotunan musulunci, na Mogadiscio, ya hadasa mutuwar mutane kussan 300, a yayin da, da dama su ka ji raunuka, sannan dubun dubanai mutane, sun shiga gudun hijira.