1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban tashin hankali a ƙasar Kyrgystan

April 15, 2010

An yi taho mu gama a tsakanin ɓangarorin dake adawa da juna a ƙasar Kyrgystan

https://p.dw.com/p/Mx51
Hoto: picture alliance/dpa

Harbe - harben bindigogi a birnin Osh dake yankin kudancin Kyrgystan sun janyo cikas ga gangamin da magoya bayan tsohon hamɓararren shugaban ƙasar Kurmanbek Bakiyev suka shirya. Rahotanni suka ce, masu tsaron tsohon shugaba Bakiyev, sun yi ta harbin albarussai a iska a yayin da magoya bayan shugabar wucin gadin ƙasar suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin gangamin magoya bayan hamɓararren tsohon shugaban ƙasar. Bayan hakane kuma, suka ɗauke Bakiyev zuwa cikin wata mota, kana masu tsaron nasa suka yi awon gaba da shi. Hamɓararren shugaban, wanda ya fice daga babban birnin ƙasar a kwanakin baya bayannan, biyon bayan kissar das aka yiwa wasu mutane da dama sakamakon jerin zanga - zangar nuna adawa da gwamnatin da suka gamu da fushin sojoji da 'yan Sanda, rahotanni sun nunar da cewar, da yammacin jiya Laraba ne ya yi magana da Frime Ministan Rasha Vladmir Putin ta wayar tarho.

Ofishin Mr Putin dai ya yi na'am da batun tattaunawar, amma bai yi wani ƙarin bayani akan mihimman lamuran da tattaunawar tasu ta mayar da hankali akai ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu