Ci gaban tashe tashen hankulla a Irak | Labarai | DW | 24.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban tashe tashen hankulla a Irak

Gwamnatin ƙasar Irak ta tsawaita dokar hana hita dare, da ta kafa jiya a sakamakon tashe tashen hankullan da su ka ɓarke tsakanin yan sunni da yan schi´a.

A ranar yau juma´a, dokar ta haramta yawo a a birnin Bagadaza,da wasu sauran birane 3, har zuwa karfe 4 na yamma.

Sanarwar da gwamnatin ta hiddo, na nuni da cewar an yi hakan ne, da nufin riga kafi ga saban rikicin da kan iya barkewa a yau juma´abayan hitowa daga sallar juma´a.

Jami´an tsaro sun samu izini buɗe wuta ga duk wanda ya taka wannan doka.

Daga farkon rikicin ranar laraba da ta wuce, zuwa yanzu kimanin mutane 200 su ka rasa rayuka, sannan massalatai da dama daga ɓangorin 2, su ka fuskanci hare hare.

Hukumomi ƙasar Iraki da wasu miryoyi daga sassa daban daban na dunia, na ci gaba da ban haƙuri, ga al´ummar Iraki, ba tare da cimma buri ba.