Ci-gaban Taron Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) a Brussels | Labarai | DW | 29.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci-gaban Taron Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) a Brussels

A taron da take yi a birnin Bruessels na ƙasar Beljiyam, Ƙungiyar Tarayyar Turai ta buƙaci rage kasafin kuɗinta

default

Zauren taron EU a birnin Brussels

Yau ce rana ta biyu ta taron kolin Ƙungiyar Tarayyar Turai ke gudana a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam-inda ta mai da hankali kan buƙatar ƙayyade kasafin kuɗinta. A jiya alhamis ne shugabannin ƙasashen ƙungiyar guda 27 suka amince da yin gyaran fuska ga yarjejeniyar Lisbon da ke tafiyar da harkokin ƙungiyar, domin kauce wa fuskantar wata matsala ta bashi. Shugabannin sun yarda cewa akwai buƙatar kafa wani tsari na dindindin da zai rinƙa kula da matsalolin bashi da ka iya addabar ƙasashe, ya kuma gindaya sharuɗa masu tsauri game da kasafi. Amma ƙasar Jamus ta gaza samun goyon baya game da shawarar da ta gabatar ta dakatar da haƙƙin kaɗa ƙuri'a ga duk wata ƙasa ta za ta wuce gona da iri wajen kashe kuɗi. Har yanzu shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel na kyautata fata game da nasarorin da aka cimma. Manufar ƙasashe mambobin Ƙungiyar Tarayyar Turai dai ita ce zayyana wani shiri da zai gindaya sharuɗa akan kasafin kuɗin ɗaiɗaikun ƙasashe kafin wani taro da za su yi a watan Disamba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi