Ci gaban shari´ar yan adawa a kasar Ethiopia | Labarai | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban shari´ar yan adawa a kasar Ethiopia

A ƙasar Ethiopia, an koma shari´ar mutanen nan, 129 da su ka haɗa da yan adawa da yan jarida, da hukuma ta tsare, tun watan november da ya wuce a sakamakon zanga zangar da aka gudanar, ta wasti da sakamakon zaɓen yan majalisun dokokin ƙasar.

Idan ba a manta ba a watan juni ne an shekara ta 2005 a ka shirya zaɓɓukan yan majalisun dokoki a ƙasar Ethiopia, zaɓen da jam ´iyar Praminista Meles Zenawi ta lashe.

Gwamnatin na tuhumar wannan mutane da kitsa maƙarƙashiyar juyin mulki.

Ƙungiyar kare haƙoƙin bani Adama ta Amnisty International, ta yi watsi da zargin da ake wa mutanen, ta kuma yi kira ga gwamnati, ta sallame su ba tare da bata lokaci ba.

A ɗaya gefen, Amnisty International, ta yi kira ga hukumomin Ethiopia su dasa aya, ga baƙin halin su na tauye haƙƙoƙin yan jarida.

Tun fara wannan shari´a a watan desember da ya wuce, a karro na farko,ƙungiyar gamayya turai, ta tura wani juju domin ya wakilce ta, hakazalika, ƙungiyar kare haƙƙoƙin jama´a, ta FIDH ko kuma IFHR.